ABNA24 : A cikin wani wani bayani dakarun sa kai na al’ummar Iraki Hashd Al-Shaabi suka fitar a yau, sun bayyana cewa ana dauki ba dadi mai tsanani tsakaninsu da mayakan ‘yan ta’adda na Daesh a cikin saharar Anbar a yammacin kasar Iraki.
Kwamandan da ke jagorantar rundunar dakarun na Hashd Al-shaabi a wannan artabu Kasim Muslih ya bayyana cewa, sun fara wannan kaddamar da wannan farmaki nea akn sansanonin ‘yan ta’addan da nufi kammala tsarkake daga wadannan mutane masu barna a bayan kasa.
Ya ce sun samu nasarar fatattakar ‘yan ta’addan daga sansanoninsu daban-daban a yankin, sun kuma samu tarin makamai a maboyar ‘yan ta’addan, da suka hada da nakiyoyi, da bindigogi masu sarrafa kansu gami da sanadaran harhada bama-bamai.
Ana zargin Amurka da wasu gwamnatocin kasashen larabawa na yankin da yunkurin sake farfado da kungiyar ‘yan ta’adda ta Daesh, domin ci gaba da kaddamar da hare-hare a cikin kasashen Iraki da Syria, bayan da aka murkushe kungiyar tare da karya lagonta a cikin wadannan kasashe, tare da taimakon kasashen Rasha da Iran, da kuma kungiyoyi irin su Hizbullah da Hashd Shaabi.
342/